logo

HAUSA

Reshen kungiyar ISIS ya sanar da daukar alhakin harin da aka kaiwa wani otel a Kabul

2022-12-13 11:26:59 CMG Hausa

Reshen kungiyar masu tsatsauran ra’ayi ta ISIS, ya sanar da daukar alhakin harin da aka kai a wani otel a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Da yammacin jiya ne, aka kai harin bom kan wani otel a Kabul, inda mahara 3 suka gamu da ajalinsu nan take, yayin da wasu 'yan kasashen waje guda biyu suka jikkata.

Tun bayan da 'yan Taliban suka karbi mulkin Afghanistan a watan Agustan 2021, reshen Khorasan na kungiyar masu tsarsauran ra'ayi, ya kaddamar da wasu hare-haren ta'addanci a cikin Afghanistan, wanda ya haddasa mutuwa da jikkatar mutane da dama. Kungiyar Taliban ta Afghanistan ta bayyana cewa, ba ta yarda da kowace kungiyar nuna ta'addanci ta gudanar da ayyukan ta'addanci a kasar Afghanistan ba. (Safiyah Ma)