logo

HAUSA

An samu rahoton barkewar cutar Kyanda a Sudan ta Kudu

2022-12-12 15:28:24 CMG Hausa

Mai’aikatar kiwon lafiya ta Sudan ta Kudu ta bayyana yayin taron manema labaran da ta shirya jiya Lahadi cewa, a cikin watannin nan, an samu mutane 2471 da suka kamu da cutar kyanda yayin da 31 suka mutu a gundummomi 22 dake jihohin kasar 10, lamarin dake nuna barkewar cutar a cikin kasar Sudan ta Kudu.

Bugu da kari, ana iya samun karuwar masu kamuwa da cutar wadanda ba a bayar da rahotonsu ba, saboda dalilai na al'ada.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta fito da manufofin shawo kan cutar, ciki har da wayar da kan jama'a game da alamomi da hadarin cutar da kuma karfafa ayyukan yin rigakafi na yau da kullun a fadin kasar. Ya zuwa yanzu gwamnatin ta riga ta karfafa ayyukan yin rigakafi a cikin gundummomi guda 15 da cutar ta barke. (Safiyah Ma)