logo

HAUSA

Kwamitin tsaron MDD ya yi na’am da sanya hannu kan yarjejeniyar warware kalubalen siyasa a Sudan

2022-12-09 12:50:48 CMG Hausa

Kwamitin tsaron MDD ya yi na’am da sanya hannu kan yarjejeniyar da sassa masu ruwa da tsaki a siyasar kasar Sudan suka yi, a wani mataki na kawo karshen tirka-tirkar siyasa da ta jima tana addabar kasar.

Wata sanarwa da kwamitin tsaron MDD ya fitar a jiya Alhamis, ta yi fatan sanya hannu kan yarjejeniyar zai taimaka, wajen kawo karshen kalubalen siyasa a Sudan, tana mai kira ga sassan ’yan siyasar kasar da su shiga a dama da su a harkokin da za su taimaka wajen warware matsalolin siyasar kasar.

A ranar Litinin ne rundunar sojojin kasar Sudan, tare da jagororin fararen hula suka sanya hannu kan yarjejeniyar siyasa, wadda za ta kawo karshen dambarwar siyasa da mulkin rikon kwarya na shekaru 2 a kasar.

Mambobin kwamitin tsaron 15, sun yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar, suna masu bayyana ta a matsayin muhimmin mataki da zai kai ga kafa gwamnatin farar hula, da tabbatar tanadin kundin tsarin mulkin kasar don gane da batun wa’adin mulkin rikon kwarya, zuwa lokacin gudanar da zabukan kasar.

Kaza lika mambobin kwamitin sun jaddada muhimmancin samar da kyakkyawan yanayi na warware batutuwa ta hanyar lumana, da tattaunawa da dukkanin sassa.

Har ila yau, an amince da bukatar ci gaba da samar da karfin gwiwar aiwatar da matakai, da kira ga sauran sassan siyasar kasar da har yanzu ba su shiga yarjejeniyar ba da su yi hakan, tare da jaddada muhimmancin ba su damammaki na shigar da su yarjejeniyar. (Saminu Alhassan)