logo

HAUSA

Sin ta yi nasarar harba tauraron dan adam na tattara bayanan kasa

2022-12-09 12:54:58 CMG Hausa


Da misalin karfe 2 da mintuna 31 na wayewar garin yau Juma’a ne kasar Sin ta yi nasarar harba sabon tauraron dan adam, na tattara bayanan kasa, daga tashar harba kumbuna ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin.

An harba tauraron dan adam din mai suna Gaofen-5 01A ne, ta amfani da rokar Long March-2D, ya kuma shiga falaki kamar yadda aka tsara.

Ana sa ran wannan sabon tauraron dan adam zai samar da hidimomi na tattara bayanan kasa, da tallafawa manhajoji daban daban masu nasaba da hakan, kamar na rage gurbatar yanayi, da lura da muhalli, da safiyon albarkatun kasa, da nazarin sauyin yanayi.

Bugu da kari, tauraron dan adam din zai taimaka wajen samarwa kasar Sin da ma ta sanya ido a sassan kare muhalli, da doron kasa, da yanayi, da noma, da shawo kan bala’u.

Wannan ne karo na 453 da aka yi amfani da rokar Long March, wajen harba tauraron dan adam. (Saminu Alhassan)