logo

HAUSA

Xi Ya Gana Da Shugabannin Wasu Kasashe

2022-12-09 20:13:55 CMG HAUSA

Da safiyar yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Mauritaniya Mohamed Ould Ghazouani a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya.

Xi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa gwiwar kamfanonin kasar Sin, da su shiga a dama su wajen raya kasar Mauritaniya a fannonin makamashi, da kamun kifi, da hakar ma'adinai da gina ababen more rayuwa, don amfanawa jama'ar kasar Mauritaniya.

A nasa jawabin kuwa, shugaba Ghazouani ya bayyana cewa, a ko da yaushe bangaren Mauritaniya, na tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tilo a duniya, kuma za ta ci gaba da nuna goyon baya ga matsayin kasar Sin kan batun kare hakkin dan Adam. Yana mai cewa, kasar Mauritaniya na fatan koyo daga nasarar da kasar Sin ta samu wajen gudanar da harkokin mulki da kara zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban.

Har ila a wannan rana, shugaba Xi ya gana da takwaransa na kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh a Riyadh. Inda ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana goyon bayan Djibouti wajen ciyar da “shirin raya kasar nan da shekarar 2035" gaba, da zurfafa hadin gwiwa a tashoshin jiragen ruwa, da zuba jari, da taimakawa Djibouti wajen gina wata cibiyar hada-hadar kayayyaki a yankin.

Shugaba Guelleh ya ce, Djibouti na son kara karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin, da ci gaba da sa kaimi ga ayyukan gina muhimman ayyukan more rayuwa. Bugu da kari, Djibouti za ta ci gaba da goyon bayan halastaccen matsayin kasar Sin, game da batutuwan da suka shafi muhimman muradun kasar Sin.

Bugu da kari, shugaba Xi ya gana da takwaransa na Comoros Azali Assoumani da sarki Tamim Bin Hamad Al Thani na masarautar Qatar.  (Ibrahim)