logo

HAUSA

Antonio Guterres: Ana bukatar yarjejeniyar kare teku sama da ko wane lokaci a tarihi

2022-12-09 12:53:51 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce sassan teku na fuskantar yanayi na tsukewa, don haka a halin yanzu, ana bukatar aiwatar da yarjejeniyar kare teku da aka amince da ita yau shekaru 40 da suka gabata, sama da kowane lokaci a tarihi.

Mr. Guterres ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake jawabi a zauren MDD, albarkacin ranar tunawa da cika shekaru 40, da amincewa da yarjejeniyar, wadda aka sanyawa hannu.

Babban jami’in na MDD ya kara da cewa, ya kamata a dora muhimmancin gaske game da tasirin da teku ke yi ga rayuwar mutane, kuma kamata ya yi cikar yarjejeniyar 40, ya zama wani muhimmin lokaci na tunawa da bukatar ci gaba da aiwatar da sahihan matakai, na shawo kan kalubalen dake fuskantar teku.

A shekarar 1982 ne aka rattaba hannu kan yarjejeniyar, wadda ta bude sabon babi a fannin jagorancin al’amuran da suka jibanci amfani da teku, ta kuma taimaka matuka wajen baiwa jama’a damar fahimta, da karewa, da kuma cin gajiyar teku. (Saminu Alhassan)