logo

HAUSA

Xi Jinping: Sin za ta yi kokari tare da Masar don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya

2022-12-09 10:22:11 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Masar, Abdel Fattah al Sisi a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya.

Yayin ganawar, Xi ya ce, bisa halin da ake ciki yanzu a duk duniya, da ma shiyyoyi daban-daban na fuskantar manyan sauye-sauye, yana da muhimmanci a raya huldodin Sin da Masar bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoi. Ya ce ya dace kasashen biyu su yi kokari tare, don neman cimma burin gina al’ummominsu masu kyakkyawar makoma ta bai daya, ta yadda za’a kara samar da sabon ci gaba, ga dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni.

A nasa bangaren, shugaba Sisi ya ce, ya zo kasar Sin don halartar bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da aka yi a watan Fabrairun bana a Beijing, inda ya yi shawarwari masu gamsarwa tare da shugaba Xi. Ya ce, ya ziyarci kasar Sin a wancan lokacin ne don goyon bayan kasar, da karfafa dangantaka tare da kasar. Sisi yana da yakinin cewa, a sabon wa’adin aikin shugaba Xi, dangantakar kasashen biyu za ta samu karin ci gaba, kana, kwalliya za ta biya kudin sabulu, wajen karfafa hadin-gwiwarsu a bangaren shawarar “ziri daya da hanya daya”. (Murtala Zhang)