logo

HAUSA

Wakilin MDD: Bai kamata takunkuman da Amurka ta kakaba wa Syria su hana agajin jin kai ba

2022-12-08 12:37:33 CMG Hausa

Wakilin MDD na musamman kan kasar Syria Geir Pedersen, ya bayyana a jiya Laraba cewa, bai kamata takunkuman da kasashen yamma karkashin jagorancin Amurka suka kakaba wa kasar Syria su hana ayyukan jin kai ba.

Yayin da yake jaddada cewa, kashi 90 cikin 100 na al'ummar Syria na fama da talauci, Pedersen ya shaidawa manema labarai cewa, ya sha nanata bukatarsa ga kwamitin sulhu na MDD cewa, takunkumin da aka kakaba wa Syria, bai kamata ya shafi taimakon jin kai ba.

Ya ce, babu wani takunkumin da MDD ta kakaba wa Siriya, amma akwai takunkuman da Amurka da EU suka kakabawa kasar, kuma ba shakka, duk wadannan suna daga cikin batutuwan da muke tattaunawa da gwamnatin Siriya da ma sauran kasashe."

Pederson wanda ya bayyana hakan bayan ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Mekdad, ya bukaci dukkanin bangarorin kasar Syria, da su kwantar da hankulansu, musamman a arewacin kasar, yayin da ake samun takun saka da Turkiyya.

Ya ce Syria ba ta bukatar karin yaki, face zaman lafiya, da tsarin siyasa. Ya kara da cewa, halin da ake ciki a Syria, ba abu ne da za a amince da shi ba, yayin da kusan mutane miliyan 15 ke bukatar taimakon jin kai. (Ibrahim)