logo

HAUSA

An samu nasarori da dama yayin da Sin da kasashen Larabawa suke kokarin raya shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

2022-12-08 20:33:23 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labaru na yau cewa, an kyautata tsarin raya shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” a tsakanin Sin da kasashen Larabawa, kana an samu nasarori da dama.

A watan nan, Sin da Palesdinu, sun daddale takardar fahimtar juna kan raya shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” tare, kuma ya zuwa yanzu Sin ta riga ta daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa tare da kasashen Larabawa 21, da kungiyar kawancen kasashen Larabawa.

Mao Ning ta yi nuni da cewa, Sin da kasashen Larabawa, sun gudanar da manyan ayyuka fiye da 200 a fannonin ayyukan more rayuwa, da makamashi da sauransu, ciki har da filin wasa na Lusail na kasar Qatar wanda kamfanin Sin ya gina, ake kuma amfani da shi a gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya ta wannan karo, da hanyar jiragen ruwa masu daukar kaya ta kan teku, tsakanin Sin da Sudan, da hanyar jiragen kasa masu amfani da wutar lantarki ta farko a kasar Masar, da tsarin hadin gwiwa na hakar mai da iskar gas a tsakanin Sin da kasashen Larabawa da sauransu, wadanda suka amfani jama’ar bangarorin biyu su kimanin biliyan 2. (Zainab)