logo

HAUSA

EU ta sanya sabbin takunkumai kan sojoji da jiragen yaki maras matuki na Rasha

2022-12-08 12:35:34 CMG Hausa

Hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Turai, ta gabatar da kudurin kakabawa kasar Rasha takunkumi karo na tara, wanda zai hada da daidaikun mutane da hukumomi kusan 200 da kuma katse hanyoyin kasar na amfani da jirage marasa matuka.

Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Laraba cewa, kunshin takunkuman guda 8 da aka gabatar ya zuwa yanzu, suna da tsauri, amma duk da haka, hukumar na kara matsa lamba kan Rasha.

Bugu da kari, hukumar EU ta ba da shawarar sanya sabbin hanyoyin takaita fitar da kayayyaki da muhimman sinadarai, da magungunan jijiya, da kayayyakin lantarki da na sadarwar IT wadanda Rasha za ta iya amfani da su.

Von der Leyen ta ce, EU za ta katse hanyoyin da Rasha ke bi, wajen amfani da jiragen sama marasa matuka, inda ta bayar da shawarar hana fitar da jirage marasa matuka zuwa Rasha kai tsaye, da hana fitar da su zuwa wata kasa kamar Iran, wadanda za su iya samar wa Rasha jiragen. (Ibrahim Yaya)