logo

HAUSA

An shirya dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa a Saudiyya

2022-12-07 13:38:19 CMG Hausa

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG da ma’aikatar watsa labarai ta kasar Saudiyya, sun shirya taron dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa na shekarar 2022 mai taken “Kara karfafa cudanya domin ingiza gina kyakkyawar makomar kasar Sin da kasashen Larabawa” ranar Litinin 5 ga wata a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya, inda jami’an gwamnati da wakilan kafofin watsa labarai da masana na kasar Sin da kasashen Larabawa 22 suka halarci taron.

A jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, ministan harkokin kasuwanci na Saudiyya kuma mukadashin ministan watsa labarai na kasar Majid Bin Abdullah Al-Qasabi ya yi fatan sassan biyu za su kara karfafa cudanyar al’adu yayin taron, ta yadda za a kara zurfafa zumuncin dake tsakanin al’ummar sassan biyu. Yana kuma sa ran kafofin watsa labarai na kasar Sin da kasashen Larabawa, za su taimakawa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ta hanyar tabbatar da sakamakon da za su samu yayin taron.

A nasa jawabin, shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, babban taron wakilan JKS da aka kammala ba da dadewa ba, ya kara kuzarin  hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya. Yana mai cewa, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, zai yi amfani da damar shirya taron, domin kara zurfafa cudanyar dake tsakaninta da kasashe Larabawa a sassa daban daban, da taka rawa wajen gina kyakkyawar makomar kasar Sin da kasashen Larabawa ta bai daya, da ma kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya. (Jamila)