logo

HAUSA

Morocco da Portugal sun shiga rukunin kasashe 8 da za su fafata a zagayen gasar cin kofin duniya

2022-12-07 10:17:30 CMG Hausa

Jiya Talata ne, aka ci gaba da wasan neman shiga zagayen kasashe 8 da za su fafata a gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar Qatar. Kasar Morocco ta doke Spaniya wadda ake sa ran za ta lashe kofin gasar, inda aka kammala wasan ta zama ci 3 da 0 bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida. A daya wasan kuma kasar Portugal ta doke Switzerland da ci 6:1, inda ‘dan wasan Portugal Goncalo Ramos ya jefa kwallaye uku rus.

Yanzu Portugal da Morocco za su fafata a wasan kusa da na karshe. (Jamila)