logo

HAUSA

Sin Ta Mikawa Najeriya Sabuwar Cibiyar Binciken Harkokin Noma

2022-12-07 20:30:19 CMG HAUSA

A jiya Talata ne kasar Sin ta mika ragamar sabuwar cibiyar binciken harkokin noma ga gwamnatin Najeriya, a wani mataki na tallafawa kokarin bunkasa albarkatun noma a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.

An gina cibiyar da tallafin gwamnatin kasar Sin, a garin Bwari dake kusa da birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, kuma za ta mai da hankali ga samar da horo, da kwarewar aiki a fannin fadada dabarun noma, da kuma ingiza cin gajiya daga noma, da sauya alaka daga salon gargajiya zuwa tsari na zamani, daga noman amfanin gona kadan zuwa noman hatsi mai tarin yawa, kana da yayata dabarun bunkasa ci gaban noman baki daya, a kasar dake yammacin Afirka.

Da yake tsokaci yayin bikin mika cibiyar, jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya ce gwamnatin Sin na goyon bayan Najeriya, a kokarin ta na kara bunkasa zamanantar da ayyukan noma. Jakada Cui ya kuma yi amanar cewa, baya ga damammaki da cibiyar za ta samar ga manoma, da jami’an hukumomin kasar, a daya hannun za bude kofar zurfafawa, da fadada alakar Sin da Najeriya.    (Saminu Alhassan)