logo

HAUSA

Sin na goyon bayan rawar da MDD ke takawa kan agajin jin kai

2022-12-07 11:09:54 CMG Hausa

Jiya Talata mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan harkokin agajin jin kai a fadin duniya, kuma tana aiki tukuru domin shiga harkokin, a sa’i daya kuma, tana goyon bayan rawar da MDD take takawa a aikin agajin jin kai na kasa da kasa, kana ya jaddada cewa, ya dace kasashe masu ci gaba, su samar da karin taimako ga kasashe masu tasowa sakamakon fama da bala’un halittu da suke fuskanta.

Geng Shuang ya yi tsokacin ne a babban taron MDD karo na 77 mai taken “Kara karfafa aikin sulhuntawa na MDD kan agajin jin kai”, inda ya ce, ya kamata kasashen duniya su inganta da kuma zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannin magance da rage bala’un halittu a karkashin jagorancin MDD, kuma ya dace kasashe masu ci gaba su cika alkawarun da suka yi kan aikin dakile matsalar sauyin yanayi, musamman ma wajen cika alkawarinsu na samar da kudaden tallafi na dalar Amurka biliyan 100 a kan lokaci.

Geng Shuang ya kara da cewa, ya dace kasashen duniya su nace kan manufar daidaita rikici cikin lumana, ta yadda za a kawar da rikicin jin kai daga tushe.

Hakazalika ya yi kira ga kasashe masu ci gaba, da su kara samar da taimako ga kasashe masu bukata, musamman ma kasashen Afirka wadanda ke fama da masifun jin kai sakamakon talauci mai tsanani da tashe-tashen hankula. (Jamila)