logo

HAUSA

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Shugaba Xi Zai Halarci Muhimman Taruka A Saudiyya

2022-12-07 20:57:00 CMG HAUSA

Daga yau Laraba 7 zuwa 10 ga watan nan na Disamba, bisa gayyatar Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiyya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci taron koli na farko, na Sin da kasashen Larabawa, da taron koli na Sin da kasashen kungiyar hadin kan yankin Gulf ko (GCC), wanda zai gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. Kaza lika shugaban na Sin zai gudanar da ziyarar aiki a masarautar ta Saudiyya. 

Game da hakan, yayin taron manema labarai na yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta gabatar da bayanai, inda ta ce taron kolin na farko na kasar Sin da kasashen Larabawa, wanda shugaba Xi Jinping zai halarta, shi ne aiki mafi girma cikin harkokin diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Larabawa, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, zai kuma kasance wani muhimmin ginshiki a tarihin alakar Sin da kasashen Larabawa.

Mao ta kara da cewa, kasashen kungiyar hadin kan yankin Gulf ko GCC, su ne muhimman abokan hadin gwiwar Sin a gabas ta tsakiya. Kuma cikin sama da shekaru 41 da suka gabata, alakar Sin da GCC na ta kara habaka daga dukkanin fannoni, cikin sauri da zurfafar ayyuka, inda alakar sassan biyu ke ta haifar da alheri na hadin gwiwa, a fannonin raya tattalin arziki da cinikayya, da makamashi, da hada-hadar kudade, da zuba jari. Sauran sassan sun hada da na manyan fasahohi, da harkokin samaniya, da raya yaruka da al’adu, wanda hakan ya sanya Sin din zama a sahun gaba, a fannin hadin gwiwa da kasashen gabas ta tsakiya. (Saminu Alhassan)