logo

HAUSA

Za a kira taron COP15 kashi na biyu a Montreal na Canada

2022-12-07 10:21:50 CMG Hausa

Kafin a kadddamar da taron COP15 na wakilan kasashen da suka daddale yarjejeniyar kare mabambanta halittu ta MDD kashi na biyu, shugaban babban taron kuma ministan kare muhallin hallitu na kasar Sin Huang Runqiu da babban sakataren MDD Antonio Guterres da firayin ministan kasar Canada Justin Trudeau sun yi maraba ga kasashen da suka daddale yarjejeniyar.

Jiya da safe, an kira taron ganawa da manema labarai na babban taron karo na farko, inda shugaban babban taron kuma ministan kare muhallin hallitu na kasar Sin Huang Runqiu ya bayyana cewa, a matsayinta na kasar dake shugabantar COP15, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokarin ba da jagoranci kan aikin, domin ingiza cimma matsaya guda kan wannan batu, ta yadda za a zartas da “tsarin kare halittu mabambanta na kasa da kasa bayan shekarar 2020” a yayin kashi na biyu na taron, ta yadda a karshe za a kai ga gina duniya mai zaman jituwa.

Za a kira taron COP15 kashi na biyu bisa taken “Wayewar kan halittu: Gina kyakkyawar makomar halittun kasa da kasa ta bai daya” ne a ranar 7 ga wata, agogon kasar Canada a birnin Montreal, dake zama ofishin sakatariyar yarjejeniyar. (Jamila)