logo

HAUSA

Jimilar kudin da kamfanonin samar da kayayyakin soja na Amurka 40 suka samu ya kai fiye da rabi a duniya

2022-12-06 13:55:42 CMG Hausa

Cibiyar nazari ta SIPRI ta Stockholm dake kasar Sweden, ta fitar da wani rahoto a jiya Litinin, wanda ke cewa a cikin manyan kamfanoni 100 na samar da makamai, da ba da hidima a fannin soja a duniya, kamfanoni 40 daga Amurka na cikin jerin sunayen, kuma jimilar kudin da suka samu wajen sayar da makamai a shekarar 2021, ta kai fiye da rabin na dukkan manyan kamfanonin sojan 100.

Rahoton ya ce, jimillar kudin da manyan kamfanonin kera makamai, da na ba da hidimarr aikin sojan 100 a duniya suka samu, a fannin cinikayyar su a shekarar 2021, ta kai dalar Amurka biliyan 592, wanda hakan ya karu da kashi 1.9 cikin 100 bisa na shekarar 2020. Wannan ita ce shekara ta bakwai a jere, da kamfanonin 100 suka samu cinikin sayar da kayayyaki. Cikin wannan adadi kuwa, jimilar kudin da kamfanonin Amurka 40 da ke cikin jerin suka samu ta kai dala biliyan 299. Tun daga shekarar 2018, manyan kamfanoni biyar dake kan gaba a jerin sun fito ne daga Amurka.

Rahoton ya kuma nuna cewa, galibin kamfanonin aikin soji sun fuskanci katsewar hanyoyin samar da kayayyaki a duniya, sakamakon barkewar annobar numfashi ta COVID 19 a shekarar 2021, kamar jinkirin jigilar kayayyaki a duniya, da kuma karancin kayan gyara da ake bukata da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)