logo

HAUSA

Mai aikin sa kai na koyar da yaran karkara

2022-12-06 11:20:19 CMG Hausa

Malam Yuan Hui ke nan, wanda ya shafe tsawon shekaru 10 yana aikin sa kai na koyar da yara a karkarar kasar Sin. An haifi Yuan Hui a wani karamin kauye da ke lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin, kuma ya bi iyayensa zuwa birni a lokacin da ya kai shekaru 14 da haihuwa. Don haka, ya san yadda yaran kauyuka ke matukar son a samar musu damar karo ilmi. Shi ya sa bayan da ya gama karatun jami’a a shekarar 2012, sai ya hau motar zuwa wani kauye mai talauci da ke lardin Hubei na kasar, inda ya yi shekara da shekaru yana koyar da yaran kauyen, duk da wahalar rayuwa da yake fuskanta. Hakarsa ta cimma ruwa, domin kuwa wasu dalibansa da dama sun samu damar shiga sanannun jami’o’i na kasar Sin, wadanda bayan da suka kammala karatunsu, su ma suka fara tallafawa yaran karkara ta hanyoyi daban daban.(Lubabatu)