logo

HAUSA

Japan da Koriya ta Kudu sun fita daga gasar cin kofin duniya na Qatar

2022-12-06 10:45:22 CMG Hausa

Jiya Litinin 5 ga wata ne, aka buga wasan daf da na kusa da na karshe, a gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya FIFA da ake yi a Qatar, inda kungiyoyin kasashen Asiya 2, wato na Japan da na Koriya ta Kudu suka kara da Croatia da Brazil.

Yayin wasan Croatia da Japan an kai bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma Croatia ta yi nasara da ci 4:2. Yayin da tawagar Koriya ta Kudu ta sha kashi da ci 4 da 1 a hannun Brazil.

A yau Talata kuma, za a buga karshen wasanni biyu na zagayen kungiyoyi takwas, inda Spaniya za ta kara da Morocco, kana Portugal za ta kara da Switzerland. (Mai fassara: Bilkisu Xin)