logo

HAUSA

Sin: Bai kamata hadin kan Amurka da EU ya shafi sauran kasashe ba

2022-12-05 21:22:15 CMG HAUSA

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, bai kamata Amurka da kungiyar Tarayyar Turai EU su rika tsokala sauran kasashe yayin da suke hadin kansu, musamman ma tada rikici dake shafar kasar Sin ba.

Shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ya sanar da cewa, a gun tattaunawar manyan jami’an Amurka da Turai karo na 4 kan batun kasar Sin, mataimakiyar ministan harkokin wajen Amurka Wendy Sherman da babban sakataren hukumar kula da matakan da aka dauka kan kasashen waje ta kungiyar Tarayyar Turai EU Stefano Sannino sun zargi Sin bisa wasu batutuwa marasa tushe. Game da hakan, Mao Ning ta nuna cewa, Sin na matukar nuna rashin jin dadi kan yadda Amurka da EU ke tsoma baki a harkokin cikin gidanta da neman shafawa mata bakin fenti.

Mao Ning ta ce, game da batun matsin lamba a bangaren tattalin arziki, Amurka tana barazana ga sauran kasashe da hana su amfani da na’urorin da kamfanonin Sin suka kera, da ma hadin kai da Sin, wannan ainihin matakin matsin lamban ne a bangaren tattalin arziki.

Ban da wannan kuma, Amurka ta gabatar da dokar sassan na’urorin laturoni da kimiyya, don hada kai da kawayenta da nufin nuna fin karfi kan kasar Sin, da ma tilasatawa sauran kasashe katse huldarsu da Sin, da tilasatawa kamfanonin Turai kaurar da kamfanonin samar da kayayyakinsu zuwa Amurka bisa dokar rage hauhawar farashin kaya, hakika wadannan duk matakai ne na matsin lamba a bangaren tattalin arziki.(Amina Xu)