logo

HAUSA

An kaddamar da ginin sabuwar hedikwatar kungiyar ECOWAS

2022-12-05 11:21:55 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne aka aza tubalin ginin sabuwar hedikwatar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin Afirka ta yamma ko ECOWAS, a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, aikin da kasar Sin za ta tallafa wajen gudanar da shi. Ana sa ran ginin zai baiwa kungiyar damar tattare ayyukanta wuri guda, sabanin yadda a yanzu kungiyar ke da ofisoshi 3 a birnin Abuja.

Shugabannin kasashen yammacin Afirka, ciki har da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, da takwarorinsa na Guinea Bissau da Saliyo, da kuma shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS Omar Alieu Touray, da jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, su ne suka jagoranci bikin aza tubalin ginin sabuwar hedikwatar.

Da yake tsokaci yayin kaddamar da aikin, jakada Cui Jianchun ya ce daukar nauyin ginin sabuwar hedikwatar ta ECOWAS da Sin ta yi, na nuni ga irin goyon bayan kasar ga ayyukan kungiyar, da ma kawancen gargajiyar dake tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka.

A nasa jawabin kuwa, shugaba Buhari ya bayyana aikin a matsayin shaidar goyon bayan Sin ga ECOWAS, kuma bayan kammalarsa, zai zamo matsugunin manyan ofisoshin ECOWAS 3, da suka hada da sakatariyar kungiyar, da kotun kasashe mambobin kungiyar, da kuma majalissar dokokin ECOWAS.

Buhari ya kara da cewa, aikin da kamfanin kasar Sin zai gudanar, zai zamo masaukin kasashen yankin yammacin Afirka baki daya, wanda zai wakilci hadin kai da ’yan uwantaka tsakanin kasashe mambobin kungiyar, zai kuma alamta karin aniyar mambobin kungiyar game da samar da ci gaba da dinkewar yankin.

Shi kuwa shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS Omar Alieu Touray cewa ya yi, wannan rana ce mai muhimmancin gaske a tarihin kungiyar ECOWAS. Ya kuma jinjinawa gwamnatin kasar Sin bisa goyon bayanta ga kungiyar.

Alieu Touray ya kara da cewa, sabuwar hedikwatar za ta baiwa hukumar gudanarwar ECOWAS, damar karbar bakuncin daukacin jami’anta a wuri guda, ta yadda hakan zai inganta ayyukanta, da rage tsadar kudaden gudanarwa, da cimma karin nasarorin aiki. (Saminu Alhassan)