logo

HAUSA

Iran ta zargi Amurka da tunzura masu zanga-zanga da nufin yi mata matsin lambar game da yarjejeniyar nukiliya

2022-12-05 10:32:08 CMG Hausa

 

Ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya ce Amurka da wasu kasashen yamma ne ke kara tunzura masu bore da nufin haifar da tarzoma, ta yadda za su tursasawa Iran din amincewa da batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta 2015.

Da yake furta hakan a jiya Lahadi, a birnin Belgrade, fadar mulkin kasar Serbia, yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na Serbia Ivica Dacic, Mr. Amir-Abdollahian ya ce "Ba za mu bari wani ya haifar mana da bore da ta’addanci a kasarmu ba".

Zanga-zanga ta barke a kasar Iran tun daga ranar 16 ga watan Satumba, bayan wata matashiya mai suna Mahsa Amini ta rasu a asibiti, ’yan kwanaki bayan da ’yan sandan kasar suka kama ta. To sai dai Iran ta ce Amurka da wasu kasashen yamma ne ke kara tunzura al’ummar kasa, tare da goyawa ’yan ta’adda a kasar baya.  (Saminu Alhassan)