logo

HAUSA

Sojojin kasar Mali sun hallaka ’yan ta’adda 66 a watan Nuwamba

2022-12-05 10:13:45 CMG Hausa

 

Sashen yada bayanai na rundunar sojojin kasar Mali ko Dirpa, ya ce dakarun rundunar sojin kasar sun hallaka ’yan ta’adda 66, yayin wasu farmaki da sojin gwamnati suka gudanar cikin watan Nuwambar da ya shude.

Kaza lika rundunar ta tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda da dama, tare da kwace ko lalata ababen hawa, da makamai, da sauran kayayyakin aiki da suke amfani da su.

Bugu da kari, sojojin kasar sun kwato dabbobi da hatsi da ’yan ta’addan suka sace, sakamakon ayyukan sojin da aka kaddamar.

Tun daga shekarar 2012, kasar Mali ke fuskantar ayyukan mayaka masu dauke da makamai, dake barazana a matakai daban daban ta fuskar tsaro, da siyasa, da ma tattalin arzikin kasar.

Kasar Mali dake yammacin Afirka, na ci gaba da fama da barazanar mayakan sa kai, da masu ikirarin jihadi, da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci, wanda hakan ya haifar da kisan dubban ’yan kasar, tare da raba da dama da matsugun nan su. (Saminu Alhassan)