logo

HAUSA

An shigar da abubuwa 47 a cikin jerin sunayen abubuwan al’adun da aka gada daga kaka da kakani da ba na kaya ba na MDD a bana

2022-12-04 17:14:34 CMG Hausa

An rufe taron kwamitin kula da abubuwan al’adun da aka gada daga kaka da kakani da ba na kaya ba na hukumar kula da ilmi da kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO karo na 17 a kasar Morocco a jiya, inda aka shigar da abubuwa 47 a cikin jerin sunayen abubuwan al’adun da aka gada daga kaka da kakani da ba na kaya ba na MDD.

A cikin abubuwan 47, akwai guda 4 dake bukatar kariya cikin hanzari, ciki har da kayan dutsen sassaka na Ahlat na gargajiya na Turkiye, da fasahar kera tukwane ta kabilar Cham ta Vietnam da sauransu. Kana an shigar da abubuwa 39 cikin jerin sunayen abubuwan dake wakiltar al’adun dan Adam da ba na kaya ba, ciki har da fasahar samar da shayin ti ta gargajiya ta Sin, wasan Wushu ta gargajiya ta Cambodia da sauransu.

Hukumar UNESCO ta bayyana a shafin internet cewa, kashi 1 cikin 3 na abubuwan da aka shigar da su a cikin jerin sunayen, suna da nasaba da kiyaye muhallin halittu da tabbatar da kasancewar bambance-bambancen halittu a duniya, wannan ya shaida cewa, kasa da kasa sun yi imani kan mayar da hankali kan aikin kiyaye muhalli. (Zainab)