logo

HAUSA

Argentina da Netherlands sun yi nasara kaiwa zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya na Qatar

2022-12-04 17:37:10 CMG HAUSA

 

Da yammacin jiya ne, aka fara buga wasan dab da na kusa da na karshe, na gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar Qatar. Argentina da Netherlands sun nuna kwarewarsu ta zama manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya, inda suka doke Australia da Amurka bi da bi, kana za su hadu a zagayen kasashe 8 da suka yi nasarar zuwa zagaye wasan kwaf daya na gasar.

‘Yan wasan Netherlands Memphis Depay, Daley Blind da Denzel Dumfries ne, suka zura kwallaye a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, inda suka doke Amurka da ci 3-1 a wasan na yammacin ranar Asabar.

Lionel Messi da Julian Alvarez ne suka jefawa Argentina kwallayen da suka ba su nasarar kaiwa wasan daf da na kusa da na karshe, bayan da Argentina ta doke Australia da ci 2-1.

Da wannan sakamako, Argentina za ta fafata da Netherlands a filin wasa na Lusail a ranar Juma'a, domin samun gurbin zuwa wasan kusa da na karshe.(Ibrahim)