logo

HAUSA

Koriya ta Kudu da Switzerland sun tsallaka zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya

2022-12-03 17:12:53 CMG Hausa

A wasannin karshe na rukunin farko, na cin kofin kwallon kafar duniya da ke gudana, a jiya Jumma’a, Koriya ta Kudu da abokiyar fafatawar ta Portugal, sun tsallaka zagaye na gaba, a yayin da Uruguay ta fita daga gasar, duk da cewa ta doke Ghana da ci biyu da nema. A dayan rukunin kuma, Kamaru ta doke Brazil da ci daya da babu, amma wannan bai hana Brazil ta tsallaka zagaye na gaba ba. Sai kuma Switzerland wadda ta doke Serbiya da ci uku da biyu.

Yanzu haka dai an kawo karshen dukkanin wasannin rukunin farko, a gasar kwallon kafar cin kofin duniya ta bana dake gudana a kasar Qatar.

A zagaye na gaba, Brazil za ta fafata da Koriya ta Kudu, yayin da Portugal za ta buga wasa da Switzerland. (Murtala Zhang)