logo

HAUSA

Morocco ta kai zagaye kwaf daya a gasar cin kofin kwallon kafan duniya na Qatar

2022-12-02 11:14:04 CMG Hausa

Kasar Morocco ta yi nasarar kaiwa ga zagayen kwaf daya, karon farko tun shekarar 1986, inda ta kasance ta farko a rukunin F, bayan samun nasara a kan kasar Canada da ci 2 da 1 a wasan da suka buga jiya Alhamis.

Nasarar da Morocco ta samu, da kuma kunnen dokin da Croatia ta yi da Belgium, ya ba ta damar zama zakara a rukunin da maki 7.  Croatia ta kare a biyu da maki 5, yayin da Belgium da Canada suka yi sallama da gasar.

Mai hosar da ‘yan wasan Morocco Walid Regragui, ya bayyana cewa komai na iya faruwa, bayan da Moroccon ta zama jagoran rukunin nasu. (Ibrahim)