logo

HAUSA

Sojojin Somaliya sun halaka mayakan al-Shabab 40 a tsakiyar kasar

2022-12-02 11:10:41 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Somaliya ta sanar da cewa, dakarun kasar dake samun goyon bayan kawayenta na kasashen duniya, sun yi nasarar kashe mayakan al-Shabab 40, a wani samame da suka kai a tsakiyar kasar.
Ma'aikatar yada labarai, al'adu da yawon bude ido ta kasar, ta bayyana cewa, wani farmakin hadin gwiwa da rundunar sojojin kasar (SNA) da kawayenta na kasashen waje suka kai a daren Laraba, an auna 'yan ta'addar a yankin Ali Foldheere da ke yankin Shabel ta tsakiya.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a Mogadishu, babban birnin kasar ta sanar da cewa, harin wani bangare ne na kokarin da ake yi na kawar da 'yan ta'adda a kasar, da kuma takaita duk wani yunkurinsu na yin zirga-zirga a yankunan da har yanzu suke zaune.(Ibrahim)