logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya yi shiru na minti daya don alhini ga mutuwar tsohon shugaban kasar Sin

2022-12-01 13:43:09 CMG Hausa

A jiya ne, mambobin kwamitin sulhun MDD, suka yi shiru na minti daya, domin tunawa da tsohon shugaban kasar Sin Jiang Zemin.
A yayin fara taron na jiya ne, zaunannen wakilin kasar Ghana a MDD Harold Agyeman, kana shugaban majalisar na watan Nuwamba, ya bayyana juyayinsu ga gwamnatin kasar Sin da al’ummar Sinawa game da mutuwar Jiang a madadin 'yan majalisar.
A madadin kwamitin sulhu, Agyeman ya bukaci dukkan wadanda suka halarci zauren majalisar, da su tsaya shiru na minti guda, domin tunawa da Jiang, wanda ya mutu jiya Laraba a birnin Shanghai yana da shekaru 96.(Ibrahim)