logo

HAUSA

Harin da aka kai a wani otel a Mogadishu ya haddasa mutuwar mutane da dama

2022-11-29 10:39:13 CMG Hausa

‘Yan sandan kasar Somaliya sun bayyana a jiya Litinin cewa, ‘yan bindiga sun kai hari kan wani otel dake kusa da fadar shugaban kasar a birnin Mogadishu, babban birnin kasar a ranar 27 ga wata, inda mutane a kalla 15 ciki har da maharin sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka ji rauni.

A cewar majiyoyin ‘yan sandan, ‘yan bindigan sun kai harin kan otel din “Villa Rosa” dake kusa da fadar shugaban kasar, da misalin karfe 8 na daren ranar 27 ga wata, inda suka yi musayar wuta da ‘yan sandan da suka isa wurin. A yammacin ranar 28 ga wata kuma, ‘yan sandan sun kwace ikon otel din da wuraren da kewayensa, inda suka harbe 'yan bindiga 5 har lahira, tare da ceton mutane 60 da aka yi garkuwa da su. Kungiyar al-Shabab ta Somaliya ta yi shelar daukar alhakin kai harin. (Safiyah Ma)