logo

HAUSA

Sin ta taya Equatorial Guinea murnar kammala babban zabe cikin nasara

2022-11-29 20:36:31 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na taya kasar Equatorial Guinea murnar kammala babban zabe lami lafiya, tare da taya shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo murnar sake lashe zaben shugabancin kasar sa.

Zhao wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na yau Talata, ya ce Sin na da imanin cewa, karkashin jagorancin shugaba Obiang, Equatorial Guinea za ta cimma manyan nasarori a fannonin gina kasa.

Zhao Lijian ya kara da cewa, bangaren Sin na dora muhimmancin gaske ga raya dangantakar dake akwai tsakanin ta da Equatorial Guinea, kuma a shirye take ta ci gaba da aiki tare da Equatorial Guinea, wajen zurfafa hadin gwiwa a sassa daban daban, da ingiza matsayin cikakkiyar huldar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu zuwa sabon mataki. (Saminu Alhassan)