logo

HAUSA

Guterres ya yi alhinin mutuwar tsohon mai kokarin wanzar da zaman lafiya

2022-11-29 09:54:36 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya nuna alhinin mutuwar Francesc Vendrell, mai shiga tsakani wanda ya taimaka wajen gudanar da manyan tsare-tsaren siyasa da zaman lafiya cikin dogon lokacin na aikin da ya shahara a MDD.

Guterres wanda ya bayyana hakan ta hannun kakakinsa, ya kuma mika sakon ta’aziya ga iyalai da kuma masoyan Vendrell. Yana mai cewa, wadanda suka yi aiki tare da marigayin, za su tuna da irin sadaukarwa da jajircewar da ya yi wajen tabbatar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa.

Jami’in na MDD ya bayyana cewa, Vendrell ya yiwa MDD hidima har na tsawon shekaru 34, tun farkon shekarar 1980. A lokacin da yake raye, ya rike mukamin mataimakin babban sakataren MDD mai kula da Amurka ta tsakiya a wani lokaci mai tsanani na turka-turkar diflomasiya, inda MDD ta goyi bayan tattaunawar da ta kai ga gudanar da zabe a Nicaragua a shekarar 1990, tattaunawar da ta kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin El-Salvador da kungiyar kwatar ‘yancin Farabundo Marti, da kuma bude hanyar samar da zaman lafiya wanda a karshe ta kai ga rikicin Guatemala a shekarar 1996.

An haifi marigayi Vendrell ne a watan Yunin shekarar 1940 a Barcelona, ya kuma mutu ranar Lahadin da ta gabata, yana da shekaru 82 a duniya. (Ibrahim)