logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwararsa ta kasar Mongoliya

2022-11-29 11:10:51 CMG HAUSA

Jiya ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwararsa ta kasar Mongoliya Battsetseg Batmunkh, wadda ta rufawa shugaban kasarta da suke ziyarar aiki a nan kasar Sin baya.

Wang Yi ya nuna cewa, huldar kasashen biyu na kara inganta, abin da ya dace da muradun kasashen biyu, kuma ya nunawa duniya tabbacin samun kwanciyar hankali. Sin na fatan kara samun hadin kai da Mongoliya tsakanin jam’iyyu 2 masu mulkin kasa da kuma kasashen 2 ta fuskar mu’amalar dabarun gudanar da harkokin kasa, da ingiza hadin kansu na samun bunkasuwa da farfadowar kasashen biyu, da kuma yin kokari tare wajen kafa kyakkyawar makomarsu ta bai daya.

A nata bangare, Battsetseg Batmunkh ta amince da abin da Wang Yi ya fada, ta kuma bayyana cewa, kasarta na goyon bayan shawarwarin da Sin ta gabatar, tana mai fatan Mongoliya da Sin za su gaggauta gduanar da ayyuka masu muhimmanci da ingiza huldar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Amina Xu)