logo

HAUSA

Sin: Ya kamata Burtaniya ta mutunta gaskiya kuma ta daina nuna rashin adalci

2022-11-29 20:08:44 CMG Hausa

Dangane da zargin da firaministan kasar Burtaniya Rishi Sunak ya yi kan manufar kasar Sin, game da riga kafin yaduwar annobar COVID-19, ciki har da duka da kame wani wakilin BBC, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Talata 29 ga wata cewa, irin kalaman na Burtaniya sun sabawa gaskiyar lamarin, tare da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, kuma Sin tana adawa da hakan.

Kakakin ya bayyana cewa, ainihin lamarin shi ne, a daren ranar 27 ga wata, domin kiyaye zaman lafiyar al’umma, 'yan sandan birnin Shanghai sun lallashi mutanen da suka taru a wata mararrabar hanya, da su bar wurin kamar yadda doka ta tanada, ciki har da 'dan jaridar BBC dake Shanghai. Ko da yake ‘yan sandan sun bayyana wa 'dan jaridar karara cewa, suna shirin lallashin mutanen da ke wurin domin su tafi, amma 'dan jaridar ya ki barin wurin, kuma bai bayyana wa 'yan sanda matsayinsa na 'dan jaridar ba. Don haka, 'yan sandan suka tafi da shi ala tilas, kana daga bisani suka umurce shi da ya tafi bayan gudanar da tantancewar da ta dace da sanar da shi doka, kuma an aiwatar da hakan ne bisa tsarin dokoki da ka'idoji.

Kakakin ya jaddada cewa, 'yan jarida na kasashen waje suna da hakkin ruwaito rahotanni bisa doka a kasar Sin, kuma dole ne su bi dokokin kasar Sin, kana ya kamata su nuna katin aikin jarida kafin su bayar da rahoto, kuma bai kamata su aiwatar da wasu ayyukan da ba su dace da matsayinsu ba, kuma hakan ya shafi duk wata kafa ta watsa labarai, kana hakan bai saba da abin da ake kira da ‘yancin aikin jarida ba.

Kakakin ya kara bayyana cewa, akwai kafafen yada labarai na kasashen waje da yawa a kasar Sin, abun tambaya shi ne me ya sa har kullum BBC ke samun matsala? Wannan batu ne da ya kamata a yi la'akari da shi sosai.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)