logo

HAUSA

An yi nasarar ceto mutane 9 da aka yi garkuwa da su a arewacin Najeriya

2022-11-29 10:40:17 CMG Hausa

Dakarun sojojin Najeriya, sun yi nasarar ceto mutane 9 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna dake yankin arewacin kasar.

Kwamishinan al’amuran tsaro da na cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata gajeruwar sanarwa, yana mai cewa, rundunar sojojin Najeriyar ta kai samame sansanin ‘yan bindigar dake yankin Chikun a jihar ranar Litinin din da ta gabata, a wani mataki na ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Aruwan ya bayyana cewa, dukkan wadanda aka ceto suna cikin koshin lafiya, kuma za a kara duba lafiyarsu kafin a sake sada su da iyalansu. Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun arce daga sansanin zuwa cikin daji, bayan musayar wuta da sojojin.(Ibrahim)