logo

HAUSA

CCPIT: cinikin waje na samun ci gaba yadda ya kamata a kasar Sin

2022-11-29 16:43:43 CMG Hausa

Yau Talata, a yayin taron manema labarai da hukumar inganta cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin wato CCPIT ta saba shiryawa, mai magana da yawun hukumar Sun Xiao ya bayyana cewa, a cikin watanni 3 na karshe a bana, kasar Sin na kara fuskantar matsin lamba a fannin cinikayyar waje. Duk da yanayin mai sarkakiya da ake kara fuskanta a waje, kana abubuwa na rashin tabbas da rashin kwanciyar hankali suna karuwa, amma cinikin wajen kasar Sin yana samun ci gaba yadda ya kamata.

Sun Xiao ya kara da cewa, za a mai da hankali sosai kan sabbin yanayin tattalin arzikin duniya da kuma sabbin bukatun kamfanonin da ke yin cinikin waje, da yin amfani da dandalin zamani, don taimaka musu samun abokan ciniki na kasashen waje.(Safiyah Ma)