logo

HAUSA

Shugaban Equatorial Guinea ya sake lashe zaben da aka yi

2022-11-28 10:21:48 CMG Hausa

Rahotanni daga Equatorial Guinea na cewa, an sake zaben shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo a matsayin shugaban kasar da ke tsakiyar Afirka.

Hukumar zaben kasar ce ta wallafa sakamakon zaben, kamar yadda shafin intanet na gwamnati ya ruwaito.

Sakamakon ya nuna cewa, jam'iyyar DEG mai mulki ta Obiang wacce ke kawance da wasu jam'iyyu 14, ta lashe dukkan kujeru 100 na majalisar dokokin kasar, da kujeru 55 na majalisar dattawa da baki dayan kujeru 588 na kananan hukumomi.

Obiang, mai shekaru 80 da haihuwa, zai ci gaba da jagorancin kasar har tsawon shekaru 7. Tuni dai ya shafe shekaru 43 a kan karagar mulki. (Ibrahim)