logo

HAUSA

Zaftarewar kasa ta halaka mutane 14 a Kamaru

2022-11-28 10:48:45 CMG Hausa

Wani hadarin zaftarewar kasa ya faru a Yaounde, babban birnin Kamaru jiya Lahadi, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 14.

Gwamnan yankin tsakiyar Kamaru Naseri Paul Bea, ya bayyana ta gidan rediyo da talabijin na kasar cewa, mutane suna gudanar da wani bikin jana'iza ne lokacin da wannan bala’i ya abku.

An ruwaito cewa, an yi bikin jana'izar ne a wani fili dake kusa wani dutse, sa’an nan kasar dake kan dutsen ta zaftare ba zato ba tsamani, ta kuma binne mutanen dake halartar bikin jana’izar.

Gidan rediyo da talabijin na kasar Kamaru ya kuma bayyana cewa, masu aikin ceto suna kokarin neman mutanen da suka tsira da rai daga bala’in, kuma ya yiwu yawan mutanen da suka mutu zai ci gaba da karuwa.(Safiyah Ma)