logo

HAUSA

An shirya gudanar da kashi na biyu na taron COP15

2022-11-28 20:19:29 CMG Hausa

A watan Oktoban shekarar da ta gabata, an yi nasarar gudanar da kashi na farko na zama na 15, na babban taron masu sanya hannu kan yarjejeniyar mabanbantan halittu (COP15) a birnin Kunming na kasar Sin. Daga ranar 7 zuwa 19 ga watan Disamba kuma, za a shirya kashi na biyu na COP15 a birnin Montreal na kasar Canada, inda Sakatariyar Yarjejeniyar kan mabanbantan halittu take.

An ce, nasarar da ta fi muhimmanci da ake sa ran cimmawa a wannan taron, shi ne a kai ga daddale "Tsarin mabanbantan halittu na duniya bayan shekarar 2020", wanda ke da nufin canja halin da duniya ke ciki na asarar ire-iren halittu, da kuma cimma daidaito tsakanin dan Adam da yanayin hallitu.

Shugabar sashen hadin gwiwar kasa da kasa na ma'aikatar kula da muhallin hallitu ta kasar Sin Zhou Guomei ta bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar da ta taka a matsayinta na kasar da ke shugabantar COP15, ba tare da yin kasa a gwiwa ba wajen inganta yunkurin yin shawarwari, da tattara ra'ayin bai daya na kasashen duniya, da kuma sa kaimi ga daddale "tsarin". (Mai fassara: Bilkisu Xin)