logo

HAUSA

Sakamakon binciken jin ra'ayin jama'a: Sama da kashi 80% na masu amsa tambaya a duniya na kiran da a kaucewa samun karuwar sabbin masu harbuwa da cutar COVID-19

2022-11-27 16:32:23 CMG Hausa

A halin yanzu dai ana ci gaba da samun bullar cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya. Tun daga farkon wannan shekara, adadin wadanda suka mutu a duk duniya sakamakon cutar ya zarce miliyan daya, kuma har yanzu kwayar cutar tana ci gaba da canzawa. A ‘yan kwanakin da suka gabata, sashen CGTN na babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, ya kaddamar da wani bincike tsakanin masu amfani da yanar gizo a duk fadin duniya, wanda sakamakon sa ya nuna cewa, sama da kashi 60% (60.44%) na wadanda suka amsa tambayoyi, sun damu matuka game da illar da cutar ke haifarwa ga lafiyar dan adam a dogon lokaci.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cewa, barkewar cutar na ci gaba da zama "lamarin gaggawa ga lafiyar jama'a da ke addabar kasashen duniya ". Hukumar ta kuma ba da shawara ga kasashe daban daban, da su ci gaba da sanya ido kan cutar, tare da sabunta shirye-shiryensu na tinkarar annobar.

Dangane da hakan, kashi 85.4% na wadanda suka amsa tambayoyin sun yi imanin cewa, ya kamata a dauki matakan hana kamuwa da cutar, kuma kashi 8.3% ne kadai suka nuna rashin damuwa dangane da halin da ake ciki. Wadanda aka zanta da su, ba su yi watsi da batun tinkarar annobar yadda ya kamata, kamar yadda kafafen yada labarai na kasashen yamma ke tallatawa ba. Akasin hakan ma, yayin da ra’ayin "yin watsi da" rigakafin cutar ke kara ta'azzara, da hadarin canzawa, da yaduwar annobar, a daya hannu cutar na ci gaba da yin illa ga al’umma a fannonin karuwar nau’o’in ta da ake da su, ta fuskar kayan aikin likitanci da karancin ma'aikata.

Kasashen da suka dauki matakan ko-in-kula game da rigakafin kamuwa da cutar a yanzu ba su ga ta zama ba, balle su kai ga cimma nasara a kwance.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)