logo

HAUSA

Hare-haren ‘yan bindiga sun halaka mutane 15 a Najeriya

2022-11-26 16:01:49 CMG Hausa

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Kaduna a tarayyar Najeriya Samuel Aruwan, ya bayyana cewa, mutane 15 ne suka gamu da ajalinsu, baya ga wasu 11 da suka jikkata, a wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a yankin arewacin kasar.

Kwamishinan wanda ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Jumma’a, ya ce, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne, suka kaddamar da munanan hare-haren a kauyuka hudu dake jihar Kaduna.

Jaridar The Nation da ake wallafawa a kasar, ta ruwaito a jiyan cewa, hare-haren sun faru ne ranar Alhamis, lokacin da ‘yan bindigar suka yiwa kauyukan kofar rago, domin karbar kudi, amma sai suka gamu da turjiya daga mutanen kauyen. Daga nan ne kuma, lamarin ya fara, kamar yadda wata majiya ta ruwaito

Hare-hare na masu dauke da makamai dai, na zama wata babbar barazanar tsaro a sassan Najeriya, lamarin dake haddasa mace-mace da ma yin garkuwa da mutane. (Ibrahim)