logo

HAUSA

Qatar ta ci kwallonta na farko a gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar

2022-11-26 16:08:15 CMG Hausa

Jiya ne, kasar Qatar dake karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafan duniya, ta ci kwallonta na farko ta hannun Mohammed Muntari, a wasan da kasar Senegal ta doke ta da ci 3 da 1 a wasansu na rukunin A a filin wasa na Al-Thumana.

Kasar Qatar dai ta yi ta matsa kaimi, inda ta yi samun damammakin zura kwallo, amma hakan bai matsa lamba sosai ga masu tsaron bayan Senegal ba. Kasar Senegal dai ta jefa kwallon na farko ne ta hannun Boulaye Dia a mintuna na 41 da fara wasa, bayan da Boulem Khoukhi ya kasa fitar da kwallon daga hadari, inda Dia ya buga ta cikin ragar Barsham.

Ana haka ne kuma, Famara Diedhiou ya kara zura kwallo ta biyu a ragar Qatar mintuna uku kacal bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Kasar Qatar ta yi ta kai hare-hare a kokarin ganin ta farke kwallon da aka zura mata, amma mai tsaron ragar Senegal Mendy ya kade kwallaye. A mintuna na 78 ne Qatar ta samu damar zura kwallo a ragar Senegal, abin da ke zama kwallonta daya tilo da ta zura a gasar.

Da wannan sakamako, Qatar ta yi rashin nasara a wasanni biyu da ta buga a gasar, inda ta zama kasa ta farko dake karbar bakuncin gasar da ta yi rashin nasara a wasan farko na gasar.

Qatar za ta kara da Netherlands a wasanta na karshe na rukuni a ranar Talata. (Ibrahim)