logo

HAUSA

Amurka tana samun riba daga rikicin kasashen Rasha da Ukraine

2022-11-26 15:14:09 CMG Hausa

Wata ‘yar jaridar kasar Faransa, ta bayyana cewa, kasar Amurka tana amfana daga rikicin dake faruwa a kasar Ukraine, ta bangaren iskar gas, da sayar da makamai da takarar masana’antu.

Shugabar sashen tattalin arziki na mujallar L’Express, Beatrice Mathieu ta bayyana yayin wata zantawa da aka wallafa jiya Jumma’a a shafin Intanet na Boursorama.com cewa, masana’antun Amurka suna shirya kwangiloli don fitar da iskar gas da ake kira “Made In USA” zuwa Turai, a wani mataki na maye gurbin gas din kasar Rasha, a kan farashi mai tsada fiye da na abokan cinikinta.

Ta kara da cewa, bayan tallafin makaman da ta baiwa Ukraine, yanzu haka masana’antun sojan Amurka, suna gaggawar sake dawo da hannun jarin sojojin kasar, da neman oda daga kasashen Turai, musamman makamai masu linzami da makaman igwa. Odan da Jamus ta yi na jirgin saman yaki samfurin F-35 daga masana’antar Lockheed Martin na kasar Amurka, ya janyo hankali matuka kan yadda Faransa da Jamus ke fakewa da wannan batu.

Mathieu ta yi nuni kan yadda Turai ke dogara sosai kan masarar Ukraine. A yayin da girbin amfanin gona ya yi kasa sosai a kasar Ukraine, masu samar da kayayyaki na kasar Amurka sun fara fitar da masara zuwa Turai.

Haka kuma rikicin makamashi, ya sanya kamfanonin Turai neman sauya matsuguni zuwa Amurka, inda ake da tabbacin samun makamashi da kuma araha. (Ibrahim)