logo

HAUSA

Sin ta kara baiwa Zimbabwe allurar rigakafin COVID-19

2022-11-26 16:11:30 CMG Hausa

Jiya Jumma’a, agogon kasar Zimbabwe, kasar Sin ta mika karin allurar rigakafin cutar COVID-19 ga Zimbabwe, inda jakadan kasar Sin dake Zimbabwe ya bayyana cewa, a halin yanzu kasashen biyu wato Sin da Zimbabwe suna gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu yadda ya kamata, kuma nan gaba za su kara habaka hadin gwiwa a fannoni daban daban.

Yawan rigakafi na wannan karo ya kai miliyan 3, uwar gidan shugaban kasar Sin Xi Jinping Peng Liyuan ce ta jagoranci aikin, wanda zai samar da allurar miliyan 1 ga mata da matasa da yara na kasar Zimbabwe domin taimaka musu a fannin kandagarkin cutar.

Yayin bikin mika alluran, uwar gidan shugaban kasar Zimbabwe Auxillia Mnangagwa ta sake nuna godiya ga kasar Sin saboda tallafin da take samarwa kasarta, inda ta bayyana cewa, Zimbabwe ta samu sakamako mai gamsarwa wajen dakile yaduwar annobar, bayan da ta yi amfani da allurar rigakafin kasar Sin. Kana tana fatan za a kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, tare kuma da godewa kasar Sin saboda rawar da take takawa kan ci gaban tattalin arzikin Zimbabwe.

Hakazalika jakadan kasar Sin dake Zimbabwe Guo Shaochun ya ce, yawan allurar rigakafin da kasar Sin za ta bai wa Zimbabwe a bana zai kai miliyan 10, kawo yanzu ta samu alluran da suka kai miliyan 5 daga kasar Sin. (Jamila)