logo

HAUSA

An mayar da sama da ’yan ci rani 200 zuwa gida daga Libya

2022-11-25 11:11:14 CMG Hausa

Ofishin dake yaki da kwararar ’yan ci rani ba bisa ka’ida ba a kasar Libiya, ya ce an yi nasarar mayar da ’yan ci rani sama da 200 gida daga kasar Libiya. Kasar Libiya dai ta kasance zango mai farin jini ga masu fatan ketare tekun Meditireniya zuwa Turai ta barauniyar hanya.

A cewar hukumar lura da ’yan gudun hijira ta MDD ko IOM a takaice, a bana kadai, jimillar ’yan ci rani 20,842, ciki har da mata da kananan yara ne aka yi nasarar cetowa daga teku, aka kuma mayar da su Libiya.

Kaza lika IOM ta ce adadin ’yan ci ranin da suka mutu a kokarinsu na tsallaka teku daga Libiya ya kai mutum 500, yayin da karin wasu 863 suka bace.

A jiya Alhamis, babban kwamishinan IOM Filippo Grandi, ya yi kira ga kungiyar tarayyar Turai ta EU, da ta sanya matakan kare lafiya da goyon bayan marasa galihu, yayin da suke aiwatar da matakai a gabobin tekun Meditereniya, da ma sauran hanyoyi da ’yan ci rani ke bi.

Cikin sanarwar da Grandi ya fitar a jajibirin bude taron ministocin cikin gidan kasashe mambobin tarayyar Turai, karkashin dandalin musamman na ministocin shari’a da harkokin cikin gida na kungiyar. Jami’in ya ce akwai bukatar aiwatar da karin matakai a matakin daidaikun kasashe, da lalubon hanyoyin tsara ayyukan ceto, da na tsugunar da bakin haure, da gaggauta damar tantancewa, da samar da tsarin samar da matsugunai ga masu matukar bukatar kariyar kasa da kasa, tare da mayar da wadanda ya dace gida cikin mutunci da kare hakkokisu. (Saminu Alhasan)