logo

HAUSA

Qatar 2022: An kawo karshen dukkan wasannin zagayen farko tsakanin kungiyoyi masu halartar gasar

2022-11-25 12:19:40 CMG HAUSA

 

Jiya Alhamis ne aka kawo karshen dukkan wasannin zagaye na farko, tsakanin kungiyoyin dake halartar gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya ta shekarar 2022 da ake bugawa a kasar Qatar.

Yayin wasan jiya, Portugal ta doke Ghana da ci 3 da 2, inda Cristiano Ronaldo dos Santos Aveiro na Portugal ya zama dan wasa na farko a tarihin gasar cin kofin duniya, wanda ya ci kwallo a kalla 1 a gasannin cin kofin duniya sau 5 a jere.

Haka kuma, Brazil wadda ake sa ran za ta iya lashe kofin, ta doke Serbia da ci 2 da nema. Kaza lika Uruguay da Koriya ta Kudu sun tashi kunnen doki maras ci. Kana kungiyar Switzerland ta doke Kamaru da ci 1 da nema.

A wasannin zagaye na 2 kuma, Portugal za ta buga wasa da Uruguay, yayin da Koriya ta Kudu za ta fafata da Ghana. Sa’an nan kungiyar Brazil za ta kara da Switzerland. (Tasallah Yuan)