logo

HAUSA

Magoya bayan kungiyar kwallon kafar kasar Ghana sun jinjinawa ’yan wasan Black Stars

2022-11-25 11:32:08 CMG Hausa

Duk da rashin nasarar da kungiyar kwallon kafar kasar Ghana ta kwasa a hannun takwararta ta Portugal, magoya bayan kungiyar ta Black Stars sun jinjinawa kwazon da ’yan wasan suka nuna, a wasan jiya Alhamis da Portugal ta lashe da ci 3 da 2.

Magoya bayan Black Stars ta Ghana, sun ce ’yan wasan kungiyar sun buga wasa da ya kasance daya daga mafiya kayatarwa tare da Portugal, duk da cewa Portugal din ce ta 8 a jerin kungiyoyi mafiya kwarewa a jadawalin baya bayan nan na hukumar FIFA.

Wasu masu sha’awar kwallon kafa a kasar Ghana, da suka kalli kwallon da kasar ta buga da Portugal a manyan allunan haska wasanni na hukumar watsa shirye-shiryen kasar, sun ce kungiyar kasar ba ta kunyata su ba, suna kuma fatan Black Stars za ta gyara kurakuran da ta yi a wasan ta na gaba na ranar Litinin. (Saminu Alhassan)