logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Kara Azama Kan Hada Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa Wajen Yaki Da Ta’addanci

2022-11-24 11:21:15 CMG HAUSA

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana jiya 23 ga wata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna himma wajen shiga ayyukan kwamitoci 3, masu nasaba da aikin yaki da ta’addanci karkashin inuwar kwamitin sulhun MDD, za ta kuma kara azamar hada gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen yaki da ta’addanci, da kyautata tsarin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, a kokarin ba da sabuwar gudummowar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

A wannan rana, kwamitin sulhu ya shirya taron gabatar da rahotanni, na hadin gwiwar hukumomi masu kula da yaki da ‘yan ta’adda. Geng Shuang ya bayyana ra’ayin kasar Sin bisa tanade-tanaden da ke cikin rahotannin da jami’an kwamitocin 3 suka gabatar.

Geng Shuang ya ce, kwamitin 1267, wani muhimmin tsarin sanya takunkumi ne kan ‘yan ta’adda karkashin inuwar MDD da kwamitin sulhu. Tawagar sa ido ta kwamitin tana bibbiyar barazanar ta’addanci, kuma rahotannin da ta gabatar sun samar wa kwamitin muhimman bayanai, tare da samar da goyon baya mai muhimmanci kan hadin gwiwar duniya wajen yaki da ‘yan ta’adda. Kasar Sin ta yaba da hakan.

Geng Shuang ya kara da cewa, kwamitin yaki da ta’addanci na ci gaba da taimakawa kasashe mambobinsa, wajen aiwatar da kudurorin kwamitin sulhu na yaki da ta’addanci, ta hanyoyin rangadin aiki a kasa da kasa, da yin musayar ra’ayoyi, da shirya taron kara wa juna sani da dai sauransu. Kana kuma, kwamitin ya yi nazari kan halin da ake ciki yanzu a duniya a fannin yaki da ta’addanci, ya inganta yin musayar bayanai dangane da yaki da ta’addanci ta yanar gizo, da yadda ‘yan ta’adda suke amfani da fasahar zamani. Ya ce kamata ya yi kwamitin ya kyautata yin amfani da albarkatun da yake da su, ya sa muhimmanci kan muhimman batutuwa, ya mai da hankali da kuma kara goyon bayan kasashen Afirka, da kasashe masu tasowa wajen inganta karfinsu.

Jakadan na kasar Sin ya ci gaba da cewa, kuduri mai lamba 1540 da aka zartas a shekarar 2004, kuduri ne na farko da kwamitin sulhu ya zartas, domin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, kana kuma ginshiki ne na kokarin da kasashen duniya suke yi na hana yaduwar makaman nukiliya. Ya ce kasar Sin ta shiga aikin dudduba kudurin daga dukkan fannoni, tana kuma goyon bayan yin amfani da damar dudduba kudurin, wajen kyautatawa da inganta tsarin aiwatar da su. (Tasallah Yuan)