logo

HAUSA

Qatar 2022: Saudiyya da Faransa sun taka rawar gani

2022-11-23 11:04:53 CMG Hausa

Yayin da ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Qatar, Faransa da Saudiyya sun nuna bajimta, inda suka lashe wasanninsu na ranar Talata.

’Yan wasan Saudiyya Saleh Alshehri da Salem Aldawsari ne suka daga ragar Argentina a wasan rukunin C, wanda aka kammala Saudiyya na da ci 2, Argentina na da kwallo 1.

Nasarar da Saudiyya ta yi kan Argentina, ta kawo karshen wasanni 36 da Argentina ta buga ba tare da an yi nasara a kanta ba. Kafin hakan, Argentina ta yi rashin nasara a karon karshen ne yayin gasar Copa America ta shekarar 2019 wanda aka buga a Brazil, inda a lokacin mai karbar bakuncin gasar Brazil ta doke Argentina a wasan kusa da kusan na karshe.

Wannan ne karon farko da Saudiyya ta yi nasara kan wata kasa daka kudancin Amurka, kuma karo na 4 da kasar ta yi nasara a wasan cin kofin duniya, cikin jimillar wasanni 17 da ta buga a gasar.

A wasan da ya gudana a filin Al-Rayyan Education City kuwa, Denmark ta tashi kunnen doki maras ci tsakaninta da Tunisia a wasan rukunin D. Kaza lika a daya wasan na rukunin C, Robert Lewandowski ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan dawowa hutun rabin lokaci, a wasan da Poland ta buga da Mexico. Da wannan sakamako ita ma Poland ta yi canjaras da Mexico.

Can kuwa a filin wasa na Al-Wakrah, Olivier Giroud na Faransa, ya shige gabe da yawan kwallaye 2, a wasannin da aka riga aka buga a wannan gasa, yayin da Faransa ta lallasa Australia da ci 4 da 1.  (Saminu Alhassan)