logo

HAUSA

An amince da kafa asusun tallafawa kasashe masu tasowa da kudaden yaki da tasirin sauyin yanayi yayin taron COP27

2022-11-21 10:44:47 CMG Hausa

Kasashe mahalarta taron COP27 da ya kammala a jiya Lahadi, sun amince da kafa wani asusun musamman, wanda zai tattara kudaden tallafawa kasashen da ke fuskantar barazanar sauyin yanayi, ta yadda za su iya tunkarar ayyukan yaki da tasirinsa yadda ya kamata.

Taron na bana, shi ne na 27 da kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD ko UNFCCC suka gudanar, kuma cikin wata sanarwa da ya fitar game da hakan, babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi na’am da kafa asusun, wanda zai samar da diyyar asara da lalacewar muhalli, yana mai fatan asusun zai yi aiki yadda ya kamata.

Mr. Guterres ya kara da cewa, taron na makwanni biyu da ya gudana a birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar, ya zamo wani ginshiki mai muhimmanci na tabbatar da adalci. Sai dai kuma ya ce kudaden da ake fatan tarawa ba za su isa ba, ko da yake tara kudin tamkar tabbatar da aniyar siyasa ce da za ta sake gina amincin da ya riga ya gurgunce.

A nasa bangare kuwa, yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, shugaban tawagar kasar Sin a taron na COP27, kuma mataimakin ministan muhalli da muhallin halittu na Sin Zhao Yingmin, cewa ya yi taron na COP27 ya yi rawar gani, wajen zakulo matakan jure sauyin yanayi, da tattara kudade na diyyar asara da lalacewar muhalli, wadanda su ne manyan abubuwan damuwa ga kasashe masu tasowa.

Kaza lika Zhao ya ce a taron na bana, kasashe masu wadata sun fito da muhimman batutuwa da suka dace, kamar batun samar da kudade, da tallafin kwarewa da kasashe masu tasowa ka iya cin gajiyar su, suna fatan kasashe masu wadata za su yi aiki tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen gina yanayi mai dorewa domin gobe.

Tun da farko, wakilin musamman na kasar Sin game da sauyin yanayi Xie Zhenhua, ya yi kira ga kasashe masu sukuni, da su ba da gudummawa, ga cimma nasarar kudurin dake kunshe cikin yarjejeniyar Paris, ta hanyar kafa asusun diyyar asara da lalacewar muhalli, domin taimakawa kasashe masu tasowa, ta yadda za su shawo kan kalubalen sauyin yanayi.

Xie ya ce kasashe masu tasowa ne za su ci gajiyar asusun, kuma bisa la’akari da karancin kudaden dake cikinsa, kamata ya yi a fara da baiwa kasashe mafiya fama da kalubalen sauyin yanayi, da wadanda ke cikin matukar bukata. (Saminu Alhassan)